Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya amince da korar masu taimaka masa na musamman guda 19 daga aiki.
A cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a yau Laraba, wannan ne zagayen farko na masu mu?amana siyasa da za a kora a yun?urin da gwamnan ke yi na rage yawan ma’aikatan gwamnati.
Daga cikin wa?anda aka kora akwai mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da babban darakta a hukumar Public Procurement Authority.
Gwamna El-Rufai ya sha suka game da korar ma’aikata kusan 7,000 da ya yi, abin da ya jawo yajin aikin ma’aikata na kwana hu?u a jihar.
Sai dai gwamnatin na kare matakin da cewa tana kashe kusan kashi 80 cikin 100 na ku?in da take samu wajen biyan albashi.Article share tools
