Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa an sako dalibai 6 da malamai 2 da ‘yan bindiga suka sace a kwalejin fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a jihar Kaduna.
‘Yan bindigar sun sako mutanen ne a cikin daren Alhamis a wani wuri da ba’a bayyana ba a Kaduna, bayan sun kwashe kusan wata daya a hannunsu.
Tashar talabijin ta CHANNELS ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na makarantar fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli, Abdullahi Shehu, yana cewa an sako mutanen ne bayan da iyayensu suka daidaita da ‘yan bindigar.
Dalibai da malaman kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ‘yan bindiga suka sako
Dalibai da malaman kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ‘yan bindiga suka sako
To sai dai bai yi cikakken bayani akan daidaitawar ba, da kuma ko an biya kudin fansa ba.
Idan za’a iya tunawa dai ‘yan bindigar sun kai hari a kwalejin fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a ranar 11 ga watan Yuni, inda suka kashe dalibi daya, suka kuma yi awon gaba da daliban da malamansu.
