Kaduna: An Hallaka ‘Yan Bindiga Ba Adadi A Dajin Rijina

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar bayan samun tabbaci daga bayanan sirri, jirgin ya?in sojin sama (NAF) ya saki ruwan bama-bamai kan sansanin yan bindiga a yankin Rijana, dake kan hanyar Kaduna-Abuja.

An ruwaito cewa harin sojojin saman ya yi raga-raga da wurin aje makamai da ginin gawurtaccen ?an garkuwa, Ali Kwaja, kuma ya hallaka dandazon yan bindiga.

Yan bindigan na amfani da wannan wurin a matsayin ma?oyarsu, da kuma kaddamar da hari kan matafiya a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wata majiya daga cikin jami’an soji ta shaida cewa harin da aka kai hanyar Kaduna-Abuja, shine ya tilasta matsa wa wajen binciken fasaha a hanyar da kuma kaddamar da harin.

Majiyar tace jami’an fasaha na rundunar soji sun gudanar da bincike kan hanyar, kuma suka gano motsin yan bindiga da ma?oyarsu, sannan suka yi musu dirar Mikiya.

“Yan bindigan dake kai mafi yawan hare-hare kan hanyar Kaduna-Abuja suna fitowa ne daga yankin Rijana-Kuzo.” “Bayan tabbatar da ma?oyar, sojojin sama na Operation Thunder Strike suka tashi jirgin yaki zuwa wurin Lokacin da suka isa wurin sun hangi yan bindigan, sannan suka musu luguden wuta.”

“Sojoji sun bi bayan wasu daga cikin yan bindigan da suka yi kokarin tserewa zuwa wani wurin, kusan kilomita 4 a kudancin Kaduna, inda suka karasa aika su lahira.”

Related posts

Leave a Comment