A daren ranar Talata ne wasu bata-gari da ba a san ko su wanene ba, suka fasa ofishin babban Alkalin kotun Dogarawa, Mai Shari’a Kabir Dabo, wanda yake shari’a tsakanin sabon sarki, Ahmed Bamalli da Iyan Zazzau, Bashir Aminu.
Sai da bata-garin suka fasa kotun, tukunna suka samu damar shiga har ofishin babban alkalin. Bata-garin sun yi kaca-kaca da wasu takardu, sun kuma kwashe kayan da alkalin yake amfani da su idan zai zauna a kotu, da wasu abubuwa da har yanzu ba a gama tantancewa ba.
Wakilin jaridar Aminiya ya bukaci tattaunawa da magatakardan kotun, mai suna Jafaru, amma abin ya ci tura, inda ya ce yanzu dai ba zai iya magana da shi ba, har sai ya tuntubi mai gidansa.
Wannan hari da aka kai a Kotun ya jefa jama’a Jihar Kaduna musanman na yankin maza?ar Zazzau cikin taraddadi da shiga ru?ani akan dalilin faruwar hakan.
Wasu na ganin harin bai rasa nasaba da shari’ar da ta gudana tsakanin Sarkin Zazzau Bamalli da Iya Bashar.
