Ka Da A Sanya Siyasa A Tsaron Jihar Zamfara – Ibilo

Alhaji Ibrahim Muhammad Ibilo
(Katukan Nasarawa Godal) a yayinda yake ganawa da manema Labaru a garin kaduna.

Ya ce, a halin da jihar Zamfara ta tsinci kanta kafin Bello Matawallen Maradun yazama Gwamna dakuma halinda jihar take a yanzu Matawalle ya chanchaci yabo

Matakin da gwamnatin tarayya tadauka na hana hakar ma’adanai da zirga-zirgar jiragen sama a yankin Zamfara abu ne dake bukatar a zurfafa bincike ba a siyasantar da al’amarinba

Yakara da cewa; duniya tasan halin da jihar Zamfara tafada tsawon shekaru abaya amma ba’a hana hakar ma’adanai da zirga zirgar jirageba sai yanzu. Kowa yasan irin kokarin da maigirma Gwamnan jihar Zamfara yakeyi akan harkar tsaro har takai dakanshi yafurta cewa idan saukarshi kujerar Gwamna zai Kawo zaman lafiya a jihar to ashirye yake zai iya aje kujerarsa

Daga karshe basaraken yayi kiraga gwamnatin tarayya data taimakawa gwamnatin jihar Zamfara domin yaki da yan’ ta’adda wajen kawo dauwa mammen zaman lafiya da cigaban jihar da al’ummarta

Related posts

Leave a Comment