Jirgin Yakin Zaben Atiku Zai Dira Jíhar Anambra Yau Alhamis

Rahoton dake shigo mana daga jihar Anambra na bayyana cewar Jam’iyyar PDP tace shiri ya yi nisa na karban ?an takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, a jihar ranar Alhamis domin gangamin yakin neman za?e.

Daraktan kamfen Atiku/Okowa na jihar Anambra, Dakta Obiora Okonkwo ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai ranar Laraba a Awka.

Yace wannan gangamin kaddamar da yakin neman zaben PDP da zai guda a Awka a yau zai tabbatar wa duniya cewa Anambra ta PDP ce gaba ?aya babu maganar wata Jami’yya.

Okonkwo yace jirgin Atiku da tawagarsa na dira a Awka zai wuce zuwa gidan gwamnati domin ziyartar gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo.

Bayan ganawa da mai girma gwamna, ?an takarar shugaban ?asa a inuwar PDP zai kuma tattauna da Sarakunan Gargajiya kar?ashin shugaban majalisar Sarakunan kudu maso gabas, Obi Alfred Nnaemeka Achebe, Sarkin Onitsha.

Game da rigingimun PDP, Mista Okonkwo yace tuni aka ha?a tawaga ta musamman kuma sun fara aiki ba kama hannun yaro domin kawo karshen kace nace tsakanin ?an takara da tawagar G5. Yace har yanzun ana ci gaba kokarin ha?a Atiku da mambobin G5 a inuwa ?aya kuma jihar Anambra ta shirya tsaf don tabbatar da nasarar Atiku a za?en 2023.

Related posts

Leave a Comment