Jiragen Ruwan Yakin China Sun Ziyarci Gabar Tekun Najeriya

Wani ayarin jiragen sojojin ruwan China bisa jagoranci wani jirgin ya?in wargaza hare-hare mai suna Nanning ya sauka a Najeriya, a wata ziyara da ba a saba ganin irinta ba daga dakarun sojin China a ga?ar tekun Atalantika cikin nahiyar Afirka.

Jakadan China a Najeriya ya yaba wa ziyarar ayarin jiragen sojin ruwan ta kwana biyar a matsayin wani muhimmin lamari cikin ala?ar ?asashen biyu, kuma rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyarta na aiki tare da China don magance barazanar tsaron teku da tabbatar da kwanciyar hankali a Mashigin Tekun Guinea, in ji wata sanarwa daga ofishin jakadancin China.

China dai ta da?e tana ?o?arin bun?asa fa?a-a-jinta a Afirka.

Jirgin wargaza hare-haren da kuma wani jirgin ya?i mai rakiya da ake kira ‘Sanya’ tare da wani jirgin dakon kaya, Weishanhu sun isa daf da ga?ar tekun Lagos a cewar wata sanarwa daga sojin ruwan Najeriya.

Yankin Afirka ta Yamma mai arzi?in man fetur, muhimmin yanki ne da ke fitar da ?anyen mai a duniya.

Yankin, musamman ma dai Angola da Najeriya na cikin manyan ?asashe masu samar da man fetur ga China. Sannan wani babban kamfanin ha?ar man fetur na China CNOOC Ltd kuma yana aikin fito da man fetur daga can ?ar?ashin tekun ga?ar Najeriya

Related posts

Leave a Comment