A daren jiya masu garkuwa da jama’a suka je har gida suka yi awon-gaba da Alhaji Surajo Body a garin Garki dake jihar Jigawa.
Ha?i?a wannan bawan Allah mutum da ya yi suna sannan ya ciri tuta ta fuskar tallafawa al’umma musamman masu ?aramin ?arfi, ko a hanya kuka ha?u dashi idan rabonka ya rantse sai ya yi maka kyautar da sai ka sha mamaki.
Mutane da yawa sun yi ittifa?in duk cikin kwaryar garin Garki babu mutum mai taimako sama da shi.
Dan haka, muke ro?on ?an uwa na kusa dana nesa dasu saka wannan bawan Allah a cikin addu’o’insu domin Allah ya ku?utar dashi cikin Salama da kwanciyar hankali.
