Jigawa: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya La?ume Rayukan ‘Yan Mata 7

Yara mata guda 7 ne, ?an shakara 10 zuwa 12, su ka hallaka a wani ha?ari na kwale-kwale da ya kife da su a kan hanyarsu ta zuwa bikin maulidi a ?auyen Gamafoi, ?aramar Hukumar Kafin Hausa, Jihar Jigawa.

Jaridar Nation ta rawaito cewa ?an matan su 10 ne su ke tafiya daga ?auyen Gafasa zuwa Gasanya a karamar hukumar Auyo domin zuwa wajen maulidi a lokacin da ibtila’in ya faru.

Dagacin Gamafoi, Haruna Gamafoi ne ya kai rahoton ha?arin ga ?an sanda.

Ya ce ha?arin ya faru ne wajen ?arfe 3:30 lokacin da jirgin ya kife da ?an mata goma amma an yi nasara tserar da uku daga ciki, inda bakwai su ka ce ga garinku nan.

An rawaito cewa ?an matan suna sauri za su tafi garin ne kuma da suka zo ga?ar kogin Gasanya amma ba su samu mai fito ba shine su ka tu?a kwale-kwalen da kan su.

Bayan ha?arin ya afku sai a ka garzaya da su asibitin Kafin Hausa inda likitoci su ka tabbatar da rasuwar 7 da ga cikinsu.

Rundunar ?an sanda ta Jigawa ta tabbatar da faruwar ha?arin.

Related posts

Leave a Comment