Mai girma Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa janyewar da ‘yan takara suke don mara wa Bola Ahmed Tinubu baya alamu ne cewa ?an takarar tasu zai yi nasara.
Ganduje ya fa?i hakan ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai a filin Eagle Sqaure, inda taron jam’iyyaer APC ke gudana yanzu haka.
“Wannan alamar nasara ce kuma ka ga yadda kowa yake murna saboda ?an takararmu Bola Tinubu ya fi sauran ‘yan takara cancanta”.
