Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF ta bayyana cewa, mutanen kudu na tsokanar ‘yan Arewa fada dan kasar ta rikice.
Kumgiyar ta jawo hankalin ‘yan Najeriya cewa kada su yanke tsammani da Kasar domin za’a shawo kan matsalolin da ake fuskanta.
Shugaban kungiyar, Audu Ogbe ne ya bayyana cewa, sun zaunane dan samo hanyar da za’a kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriya.
Shi kuwa sakataren Kungiyar, Mukhtar Aliyu cewa yayi, hare-haren da ake kaiwa ‘yan Arewa a kudu na tsokanar fada ne. Saidai yace a koda yaushe bin doka da oda shi ya fi wajan warware matsaloli.
