Tsohon Kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji DanSarauniya ya ce, wasu tantirai marasa ilimin addini da na boko ne ke juya akalar gwamnati da siyasar Kano.
Injiniya Dan Sarauniya ya bayyana haka ne ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook Inda ya ce, “Jahilci ba ado ba ne, illa ne ga rayuwa da ci gaban zaman lafiyar al’umma”.
Ya kara da cewa, “Jiha kamar Kano wadda keda Gwamna mai ilimin boko da addini da ya kai har matakin Dakta amma a ce wasu tantirai ba arabi ba boko su ne ke juya akalar lamuran mu a siyasa da rayuwa”.
Wannan magana ta Dan Sarauniya ta haifar da kace-nace inda ya fara samun martani daga masu bibiyar shafin nasa.
Ko a ranar Litinin da ta gabata ma dai Dan Sarauniya ya kalubalanci shugaban jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas da ya je ayi masa gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Batun da ya dauki hankulan jama’a musamman a kafafen sada zumunta, sai dai har kawo wannan lokaci ba a ji martani daga bangaren Jami’yyar APC ba game da wannan batutuwan da Dan Sarauniyar ke wallafawa.
Ininiya mu’azuMagaji dai ya yi kaurin suna inda akoda yaushe ba ya gani ya gyale Idan za’a iya tunawa a cikin shekarar da ta gabata ne Gwamna Ganduje ya sauke shi daga Kwamishina, biyo bayan wasu kalamai da ya yi a Facebook kan mutuwar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Malam Abba Kyari.
Bayan daga bisani ne, Gwamna Ganduje ya sake nada shi a matsayin mai sanya ido kan aikin janyo bututun gas zuwa jihar Kano.
