Shugaban Hukumar Za?e ta ?asa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ?alubalanci jami’an za?e na hukumar da ke ofishin ta na Gundumar Babban Birnin Tarayya da su tabbatar da cewa an cimma nasara a za?u??ukan da za a yi na ?ananan hukumomin yankin a ranar 12 ga Fabrairu.
Farfesa Yakubu ya fa?i haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga jami’an za?e da sauran ma’aikatan INEC da ke ofishin hukumar na gundumar a garin Abuja a ranar Laraba inda su ka tattauna kan za?en da za a yi.
Yakubu ya ce ofishin INEC na yankin Abuja bai da wani uziri da zai iya ba ‘yan Nijeriya idan ya gaza cimma nasara, domin kuwa hedikwatar hukumar ta yi dukkan abin da ya kamata ta yi wa ofishin ta na gundumar domin gudanar da wannan za?e.
Ya bayyana fatan alherin cewa da yake akwai ?wararrun jami’an za?e a ofishin INEC na gundumar wa?anda sun gudanar da za?u??uka a baya, ba su da wani uziri da za su bayar a kan gudanar da wannan za?e na ?ananan hukumomin.
Ya ce, “Mun shata layin inganci wajen gudanar da kar?a??en za?e a Nijeriya, don haka za?en gundumar Abuja ba zai kasa a hakan ba.
