Ina Neman Saurayi ?an Shekara 23 – Shugabar Zawarawan Kano

Shugabar ?ungiyar Muryar Zawara ta Jihar Kano Hajiya Altine Abdullahi ta bayyana cewa auren yaro matashi mai ?ananan shekaru da babbar mace ko yarinya budurwa mai ?ananan shekaru da babban mutum mai shekaru ba wai wani sabon abu ba ne tun ma a zamanin da balle kuma a zamanin yanzu.

Shugabar ?ungiyar Muryar Zawarawan ta bayyana hakan ne a ya yin da Jaridar Dokin ?arfe TV ta tattauna da ita ta wayar salula domin jin yadda ta ke kallon wannan batu na “Wuff” da ake yayi a tsakanin maza da mata a wannan zamani.

Hajiya Altine ta ?ara da cewa ko da ita a karan-kanta za ta iya auren yaro matashi mai ?ananan shekaru 20 zuwa 25 domin su raya Sunnar ma’aiki Annabi Muhammad (S.A.W).

Sai dai kuma Hajiya Altine ta yi ?arin haske da cewa za ta iya auren yaro matashin ne idan har ta tuntu?i ?a?anta sun amince domin samar da masalaha da ?orewar auren cikin nasara.

“Ko da ?a?an ba su yarda ba, da mace ta ha?a ala?ar banza da yaro a waje ta barwa ?a?anta abin kunya, gara ta aure yaron domin hakan bai sa?awa shari’a ba, ni kuma ba na shakkar aikata duk abin da bai sa?awa addinina ba”. Cewar Altine Abdullahi.

Shugabar ?ungiyar Muryar ta Zawarawa ta kuma ?ara da fayyace cewa ko da a tarihin Musulunci, Manzon Allah (S.A.W) ya auri yarinya budurwa wacce ya girma, sannan kuma ya auri babbar mace wacce ta fi shi shekaru. Saboda haka wannan ba wani abu ba ne, abin da ya kamata dai shi ne a yi soyayya da ?auna domin Allah ba don wani abun duniya ba.

Da mu ka tambaye ta ko miye ra’ayinta game da ?an mata da su ke kokawa cewa manyan mata na aure musu samari ?, Sai ta maida amsa da cewa ai su ma ?an matan ana yin wuf da su domin akwai manyan mutane masu shekaru da su ke auren yara ?an mata ?an shekaru 18 zuwa 25 dan haka wannan duk ba wani abu bane na aibanta juna ko zargin juna ba.

Duba da matsalolin da ake samu na ?aukewar sha’awa saboda shekaru kuwa Hajiya Altine ta bayyana cewa wannan ba wani abu bane matu?ar da soyayya a tsakani, domin ita a karan kanta za ta iya nemowa yaron da ta aura yarinya budurwa ya aura idan har ita ?in ba za ta iya biya masa bu?atar sha’awar aure ba ko kuma ta dena haihuwa. Sannan kuma duk wani namiji babba mai shekaru shi ma zai iya amfani da ?wayoyin ?ara kuzari ya gamsar da matarsa har ?arshen rayuwa ba tare da ta nemi wani ?a namiji ya biya mata sha’awar aure ba.

Related posts

Leave a Comment