Ba Za Mu Amince Maza Su Cigaba Da Danne Mu Ba – Matan Najeriya

Gamayyar Kungiyoyin cigaban Mata a Najeriya sun koka dangane da yadda Maza suka yi kane-kane a dukkanin mukamai da madafun ikon ?asar nan, yayin da su kuma Mata aka mayar dasu koma baya.

Gamayyar kungiyoyin Matan sun bayyana hakan ne a takardar da suka gabatar a wajen taron saurarar bayanai na gyaran fuska a kundin tsarin mulkin kasa dake gudana a Kaduna.

Matan sun bukaci da a ware Jihohi biyu cikin guda 36 da ake dasu a Najeriya ga Mata, sannan a gwamnatin tarayya bangaren majalisar wakilai ya zamana suna da cikakken wakilci, sannan a ware musu kujerar Sanata guda daga cikin Sanatoci uku da ake dasu a kowace jiha a ?asar.

Matan sun bayyana cewar lokaci ya yi da Mata za’a dama dasu a dukkanin ?angarori na kasar saboda sun cancanta ta kowanne fanni, bisa ga haka suke neman aba Mata kaso 35 cikin 100 na mukaman da ake bayarwa a gwamnatin tarayya.

Related posts

Leave a Comment