Iyalan fitaccen mai fitowa a wasan kwaikwayon Hausa na barkwanci a shekarun baya Usman Baba Pategi da ak fi sani da Samanja sun ce yana nan da ransa bai mutu ba.
A ranar Alhamis ne aka fara ya?a labarin rasuwar Samanja Mazan-Fama a shafukan sada zumunta a Najeriya.
Amma a wata hira da BBC Hausa ta yi da babban ?ansa Yusuf Usman, ya bayyana cewar ko da La’asar ?innan sun yi hira da baban nasa kuma lafiyarsa ?alau.
Yusuf ya bayyana rashin jin da?insa kan yadda aka ?ir?iri labarin ?arya na mutuwa aka danganta da mahaifinsa.
Samanja dai ya shahara sosai a fina-finai da yake yawan fitowa kuma a matsayin soja a shekarun 1980.
A yanzu yana zaune a cikin garin Kaduna tare da iyalinsa cikin koshin lafiya.
