Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Uwar gidan shugaban ?asa, Aisha Muhammadu Buhari, ta shiga jerin yan Najeriya dake kiran a ?auki tsattsauran mataki kan makasan Hanifa Abubakar.
Hanifa Abubakar ‘yar kaminin shekara 5 a duniya, ta rasa ranta ne a hannun shugaban makarantarsu, wanda ya yi garkuwa da ita kuma ya kashe ta sannan ya binne gawarta a wani wuri cikin Makarantar.
Uwargidan shugaban ?asa ta sanya wani gajeren bidiyo a shafinta na Instagram, wanda babban malamin addninin musulunci, Sheikh Abdallah Gadon ?aya, yake neman a ?auki mataki kan lamarin.
A cikin kalamansa, Malamin yace ran makashin Hanifa bai fi na wacce ya kashe ba, dan haka shi ma a kashe shi kowa ya gani domin zama darasi ga ‘yan baya.
Gadon ?aya yace: “Don haka kamata ya yi a kashe shi, kamar yadda ya halaka ?aramar yarinya. Kuma idan za’a kashe shi, kamata ya yi a fito fili kowa ya gani, domin gobe kar wani ya maimaita.”
Aisha Buhari ta nuna goyon bayanta kan kalaman malamin na raba makashin Hanifa da duniya, kuma ta jawo hankalin sufeta janar na yan sandan ?asar nan. A kalamanta, uwar gidan shugaban ?asa tace, “Muna goyon bayan hukuncin kisa kan Malamin.”
A ranar 2 ga watan Disamba, 2021, shugaban makarantar yara dake Kwanar Dakata, ?aramar hukumar Nasarawa, cikin kwaryar birnin Kano, Abdulmalik Tanko, ya sace Hanifa Abubakar.
Jami’an tsaro sun samu nasarar kame Tanko, wanda ya karbi N100,000 a wani sashi na miliyan N6m da ya nema kudin fansa daga iyalan yarinyar. Shugaban makarantar ya kashe ?aramar yarinyar da maganin ?era na N100 kacal, kamar yadda ya tabbatar wa hukumar ‘yan sanda.
