Hukumar NBC Ta Haramta Sanya Addini Da Kabilanci A Shirye-Shiryen Siyasa

Hukumar kula da kafofin ya?a labarai ta ?asa NBC ta ce ta lura da yadda ake sanya abubuwan da suka shafi addini da ?abilanci da kuma kalaman tunzura jama’a a shirye-shiryen siyasa da ya?in neman za?e a yayin da ake fuskantar za?en gwamnoni a ?asar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce yin hakan ba zai zame wa ?asar alkairi ba.

Hukumar ta ce doka ta tanadar da cewa dole kafofin ya?a labarai su taimaka wajen jaddada hadin kan ?asa tare da taimaka wa wajen inganta dimokradiyya.

Haka kuma sanarwar ta yi kira ga kafofin ya?a labaran ?asar da su yi amfani da kafofin nasu wajen da?ile wannan a?ida, da kuma kalaman tunzura jama’a da za su iya kawo barazana ga ha?in kai da dimokra?iyyar ?asar.

A cewar sanawar duk da cewa ana ?arfafa wa kafofin ya?a labarai gwiwwa wajen bai wa ‘yan ?asa damar bayyana ra’ayoyinsu, wa?anda ba kalaman ?iyayya ko na cin zarafin juna ko na tunzura jama’a ba, ya kamata kafofin ya?a labaran su san cewa za su yi hakan ne kawai ta hanyar da ta dace.

Related posts

Leave a Comment