Harin Kurkukun Abuja: Masu Tattara Bayanai Sun Bani Kunya – Buhari

Shugaban ?asa Buhari ya bayyana cewa hukumomin tattara bayanan sirri sun ba shi kunya bayan harin da aka kai a gidan yarin Kuje da Abuja.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin ziyara da ya kai gidan yarin ranar Laraba, kamar yadda ya sanarwar da mai taimaka masa kan ya?a labarai Garba Shehu ya fitar.

“Hukumomin tsun ba ni kunya. Ta yaya ?an ta’adda za su shirya, su kai hari ga wurin da jami’an tsaro suke kuma su gudu?”

“Ta yaya jami’an tsaron da ke gidan yarin suka gaza da?ile harin? Fursunoni nawa ne a ciki? Guda nawa ne za a iya bayar da bayaninsu? Jami’ai nawa ne ke aiki lokacin da lamarin ya faru? Nawa ne ke ?auke da makami?

“Masu gadin gidan yarin sun hau kan hasumiya? Shin kemarar tsaro tana aiki?” Duka wa?annan tambayoyin shugaban ya yi su a gidan yarin.

Bayan haka shugaban ya ce yana bu?atar a kai masa cikakken bayani kan yadda wannan lamarin ya faru.

Related posts

Leave a Comment