Harin Jirgin Abuja: ‘Yan Bindiga Sun Saki Karin Fasinjoji 7

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar mai shiga tsakanin gwamnati da ‘yan bindigar da suka yi fashin jirgin kasan Abuja-Kaduna Tukur Mamu ya bayyana cewa ?an bindiga sun saki ?arin wasu fasinjojin jirgin kasa da suka yi garkuwa dasu.

Wa?anda aka saki sun ha?a da Muhammad Daiyabu Paki, Bosede Olurotimi, Abubakar Zubairu, Alhassan Sule, Sadiq Ango Abdullahi, Aliyu Usman Muhammad Abuzar Afzal dan asalin kasar Pakistani.

Mamu ya ce sai da suka yi tafiyar kilomita 40 a cikin daji kafin nan suka gamu da sojojin da suka raka su zuwa Kaduna.

Har yanzu akwai sauran fasinjoji tsare a hannun ?an bindigan wanda ke jiran tsammani.

Fasinjojin sun shafe kwanaki sama da ?ari tsare a hannun ?an bindiga.

Related posts

Leave a Comment