Har Yanzu Babban Banki Bai Wadatamu Da Sabbin Takardun Naira Ba – Bankuna

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Bankunan kasuwanci a Najeriya sun mayar da martani kan i?irarin babban bankin Najeriya CBN kan cewa ya bai wa bankunan kasuwanci isassun sababbin ku?a?e kawai sun ri?e su ne.

An ruwaito cewa Mrs Hadiza Ambursa wadda jami’a ce a Access Bank, wadda ta wakilci manajan darakta ta ce, an ba su kashi 10 ne kacal cikin 100 na ku?in da suka bai wa CBN.

A yayin wani zama da wakilan bankunan kasuwanci suka yi da kwamitin majalisar tarayya, ma’aikaciyar ta ce “Ba ma samun ku?in cikin gaggawa kamar yadda muke bu?ata. Muna samun kashi 10 ne kawai cikin 100 na abin da muka kai wa CBN. Muna biya muna kuma kar?a kudi. Kuma a gefe ?aya muna sanya ku?in a ATM.

Mista Jimoh Garuba wanda wakilin Sterling Bank ne, yace bankin nasu yana samun ku?i daga CBN amma ba ya kai wa yadda zai isa ga bu?atun kwastomominsa.

Yace, bankinsu na kar?ar abin da bai gaza naira miliyan 150 ba daga CBN kowanne mako su rabawa reshinansu da ke Abuja.

Ya ?ara da cewa a Kaduna, bankinsu ya ?arbi naira miliyan 150 a kowanne mako ya kuma raba su ga duka rassansa da ke jihohi 36 na tarayya.

Ya ce a Kano, “ana bamu naira miliyan 100 ne a mako, ba za mu iya komau da su ba bayan sanyawa a na’urar ATM”.

Ms Arerepade Akagwe, wadda wakilin United Bank for Africa (UBA) ne, ta ce ta karbi kashi 70 na tsofaffin ku?in da ta bai wa CBN.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN akwai sauran bankuna irinsu Guarantee Trust Bank (GTB), ECO bank, Lotus Bank da Fidelity da suka amince sun kar?i kimanin kashi 60 na tsafaffin ku?in da suka mayar wa CBN.

Shugaban kwamitin ?an majalisar wakilai alhassan Ado-Doguwa ya ce gayyatar da aka yi wa bankunan ba abin ta da jijiyar wuya ba ne, yanayi ne na bincike kan abin da ya shafi al’umar Najeriya.

“Muna da bu?atar sanin gaskiya kan ainihin i?irarin da bankunan kasuwanci suke yi na cewa CBN bai bayar da sabbin ku?i ba, da kuma na CBN da ke cewa ya bayar da kudaden da suka kamata.

Related posts

Leave a Comment