Duk da cewar harkar fim ba ta tafiya saboda Mutuwar da kasuwar ta yi, to ni tauraruwa ta ba ta fadi ba, domin har yanzu ina nan ina ci gaba da harkokin da na saba yi a baya.
Wannan Kalaman sun fito ne daga bakin fitaccen jarumin Barkwanci Aminu Ali Baba kofar Nassarawa, wanda aka fi sani da Aminu Baba Ari, a lokacin da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Dimokuradiyya dangane da rashin ganin sa, a harkar fim a wannan lokacin.
Jarumin ya ce gaba da cewar, “A yanzu harkar ta koma online, ko kuma fina-finai masu dogon zango, to a baya na bude shafi na na YouTube, ina saka gajerun fina-finan Barkwanci, amma sai na tattara na watsar, amma dai su masu shafukan YouTube din, suna kira na ina yi musu aiki suna biyana, amma dai na yi na saka a shafina, to wannan ba na yi, don haka ina yin talluka ne, na kamfanoni da harkar siyasa, don ka ga tun da harkar ta zama haka, to ba za a zauna ba, don na koma wani bangaren duk da dai da sunan fim din na ke gudanar da sana’ar tawa, don haka ina nan ana damawa da ni.” Inji shi.
