Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwa da labarin yanka Manoma da Boko Haram suka yi a Borno, jiya.
Ya bayyana cewa wannan abin Allah wadai ne da kuma ya taba duka Najeriya. Yace yana jajantawa iyalan mamatan da kuma fatan Allah ya jikansu.
Shugaban a sakon da ya fitar ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, gwamnati ta baiwa jami’an soji dukkan abinda ya kamata dan tabbatar da tsaro.
Matsalar tsaro dai na cigaba da ?azancewa a sashin Arewacin Najeriya, rayukan jama’a musamman Manoma na ?ara shiga cikin mawuyacin hali sakamakon kisan da ‘yan ta’adda ke yi musu babu dare babu rana.
A yankin Jihohin Arewa maso yamma a Jihohin Katsina da Zamfara, ‘yan Bindiga har haraji suke ?a?abawa Manoma su biya kafin a basu dama su gudanar da aikace-aikace a gonakin su.
Halin da yankin Arewa ya samu kan shi ciki a wannan zamani ya munana matu?a, wannan na daga cikin dalilan da ya sanya a kwanakin baya mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana yankin a matsayin inda ke da hatsarin zama a kasar.
