Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu Akan Pantami

?ungiyar gwamnonin arewa ta nesanta kanta da duk wata kalar cece-kuce da wasu ‘yan Najeriya keyi kan kalaman da Ministan Sadarwa Pantami yayi a baya masu nasaba da harkar tsaro.

A ruwaito ?ungiyar gwamnonin arewa sun bayyana cewa ba laifi bane idan Ministan sadarwa da tattalin arzi?in zamani ya fa?i ra’ayinsa. A jawabin ?ungiyar tace Ministan ya wanke kansa inda yayi martani a kan lamarin, kuma martaninsa ba ya bu?atar bincike ko kuma ?in amincewa domin yayi cikakke bayani.

“Ministan ya fito ya kare kansa, kuma jawabinsa baya bu?atar bincike ko kuma ?in amincewa.” Hakanan ?ungiyar gwamnonin tace ta gano wani labari da a ke ya?awa a kafafen sada zumunta domin ?atawa gwamnonin yankin arewa suna, inda ake ya?a jita-jitar cewa suna goyon bayan kalaman da Dr. Pantami yayi a baya.

?ungiyar tayi kira ga al’umma da suyi watsi da duk wani labari da suka gani a na ya?awa a kafafen sada zumunta domin a ?ata musu suna.

Hakanan, Isa Pantami, yayi zargin cewa duk wa?annan abubuwan dake faruwa akansa shirayayyu ne, kuma an shiryasu ne domin a ?ata masa suna.

Related posts

Leave a Comment