Baya ga shirinta na ciyo bashi daga ciki da wajen kasar don aiwatar da kasafin kudin shekarar 2021, gwamnatin Najeriya ta tabbatar da kudirinta na sayar da wasu kadarorin kasar don cimma burinta a kan kasafin kudin.
Gwamnatin ta kuma ce za ta sayar da wasu kadarorin bangaren da ba su da nasaba da man fetur a matsayin kari a kan hanyoyin samun kudaden tafiyar da kasafin kudin.
Wannan na kunshe ne a wani jawabin da ministar kudin kasar Zainab Ahmed ta gabatar wa masu ruwa da tsaki a kan abin da ya shafi kasafin kudin na shekarar 2021.
A watan Disamban shekarar da ta gabata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin shekarar 2021 da ya kai naira tiriliyan 13 da biliyan 58, wato ya dara na bara da naira biliyan 505.
Wannan mataki da Gwamnatin ta bayyana aniyar ?auka dai ya haifar da surutai a tsakanin jama’ar Najeriya, inda ake ganin kamar ?asar ta shiga cikin wani yanayi na tsaka mai wuya da ba’a ta?a shaida gani a tarihin kafuwarta.
