A ranar Talata, 15 ga watan Disamba, 2020, gwamnatin tarayya ta ce ta karbo aron kudi daga Sin domin aikin jawo gas da ake yi a Najeriya.
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ci burin kammala jawo gas tun daga garin Ajaokuta zuwa Kaduna har jihar Kano kafin nan da 2023.
Jaridar Vanguard ta ce Ministar tattalin kudi na kasa, Zainab Ahmed, ta bayyana wannan a lokacin da ta kai ziyara zuwa inda ake aikin.
Ministar tarayyar ta bibiyi sashen wannan aiki da kamfanin Oilserv Nigeria Limited ya ke yi tsakanin Ajaokuta zuwa Abuja a ranar Talata.
Zainab Ahmed ta bayyana cewa ta na sa ran za a kammala wannan aiki a lokacin da aka tsara domin kuwa kamfanin Oilserv Nigeria sun dage.
A cewar Ministar, amfanin wannan aiki na kawo gas ya hada da samar da aikin yi ga matasa, sannan a buda hanyar habaka tattalin Najeriya.
