Gwamnatin tarayya ta umarci ma’aikatan gwamnati da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.
Shugaban kwamitin Shugaban ?asa na Ya?i da Korona, PTF, Boss Mustapha da jagora na ?asa, Sani Aliyu ne suka sanar da haka yayin taron manema labarai ranar Talata.
Ma’aikatan gwamnati na mataki 12 zuwa sama da wa?anda ke yin ayyuka masu matukar muhimmanci ne suke zuwa aiki.
Amma a yanzu kwamitin ya umurci dukkan ma’aikata na ?asa da mataki na 12 su koma bakin aiki. Amma duk da haka ta umarci ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin da ke karkashin gwamnati su raba ranakun da ma’aikatan za su rika zuwa aiki don gudun cinkoso.
