Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa a yayin da wa’adin da Hukumar Aikin Hajji ta sanya na biyan cikon kudin aikin hajjin bana yake cika zuwa karfe 12 na dare, sauki ya zo ma wasu maniyyata sakamakon Gwamnatin Tarayya da jihohin Kebbi, Kano, Kogi da Ogun suka ba da tallafi ga maniyyatan su don cika kudin aikin hajjin bana.
Duk da haka dai, wasu maniyyatan sun ci gaba da neman Hukumar Walwala Da Jin Dadin Mahajjata na Jihohinsu da su mayar musu da kudin da suka ba da ajiya saboda ba za su iya cika N1.9m kamar yadda Hukumar Aikin Hajji Ta Kasa ta sanar a ranar Lahadi.
Yayin da wasu kuma ke kokarin cikawa da kansu.
Ya zuwa wannan lokacin dai babu tabbacin za a daga wa’adin da aka sa na rufe karbar cikon kudun aikin hajjin.
Haka kuma, wata majiya ta tabbatar ma da Jaridar Daily Trust cewa, Gwamnatin Tarayya ta saki N90 Billion don tallafa ma aiki hajjin bana zuwa Kasar Saudiyya.
Majiyar ya sake cewa, ba dan wannan tallafin na gwamnatin tarayya ba, da kowane maniyyaci sai ya kara akalla N3.5 Million a kan kudin da ya ajiya na N4.9 Million.
Haka zalika, wani babban ma’aikaci a fadar shugaban kasa ya tabbatar da ba da wannan tallafin don gudanar da aikin hajji.
