Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya bada wa’adin mako daya ga makiyaya su bar kungurumin jejin da ke cikin jiharsa.
Gwamnan Ondo ya bada wannan wa’adi ne a yunkurin da yake yi na kawo karshen matsalar garkuwa da mutane da sauran ta’adin da ake yi a jihar.
Sanarwar Rotimi Akeredolu ta fito ne kai tsaye a shafinsa na Twitter, a ranar Litinin 18 ga watan Junairu. 2021.
Rotimi Akeredolu a jawabin na sa yake cewa an maida jejin jihar Ondo wuraren tafka ta’adi, don haka a matsayinsa na gwamna ya dauki wannan mataki a yau.
Yace: “A yau, mun dauki babban mataki na kawo karshen matsalar garkuwa da mutane, da sauran danyen ayyukan da ake yi da muka samu labari a rahotonmu.
“Ana alakanta wadannan munanan abubuwa da wasu miyagu da ke fakewa da sunan makiyaya.” Inji gwamnan.
“Wadannan miyagu sun maida jejinmu wuraren ajiye wadanda suka yi garkuwa da su, suna tattauna yadda zasu karbi kudin fansa da yin sauran laifuffuka.”
Daga cikin matakan da aka dauka, za a bar duk wasu jeji nan da kwana bakwai. An kuma haramta kiwo da dare, sannan an hana dabbobi yawo a manyan tituna.
Gwamna ya kuma hana kananan yara kiwo, sannan bayan wannan wa’adin ya cika, gwamnati za ta bada damar duk mai bukatar yin kiwo, ya yi rajista da hukuma.
