Gwamnatin Buhari Ce Ta Jefa ‘Yan Najeriya Halin Kuncin Da Suke Ciki – Akpabio

IMG 20240310 WA0183

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bu?aci ?an Najeriya da su ?ara ha?uri da shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu. Akpabio ya bayyana cewa Tinubu yana ?o?arin gyara tattalin arzi?in ?asar nan ne wanda ya zargi Gwabnatin Bahari da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, tayi masa babban gi?i.

Tattalin arzi?i ya ta?ar?are Akpabio ya yi nuni da cewa Shugaba Tinubu ya gaji tattalin arzi?i ne wanda ya kusa dur?ushewa inda yanzu yake ?o?arin yin amfani da basirarsa wajen ceto shi, cewar rahoton jaridar Leadership.

Shugaban majalisar dattawan shima wanda EFCC ke Zargin sa da da sace kudaden jiharsa ya yi wannan ro?on ne a filin wasa na Ikot Ekpene da ke jihar Akwa Ibom a ?arshen mako a wajen wata liyafa da aka shirya masa tun bayan zamansa shugaban majalisar.

Ya bayyana cewa yana kan bakansa na cewa Emefiele ne babban mai laifi kan halin da tattalin arzi?in ?asar nan yake ciki duk kuwa da ?arar da tsohon gwamnan na CBN ya kai shi kotu saboda cewa hakan.

Tinubu zai gyara tatttalin arzi?i Ya nuna ?warin gwiwarsa cewa Tinubu zai dawo da tattalin arzi?in ?asar nan kan turba kamar yadda ya yi a jihar Legas lokacin da ya ri?e mu?amin gwamna

Related posts

Leave a Comment