Gwamnan Sakkwato Ya Sa Hannu A Dokar Da Ta Rage Karfin Ikon Sarkin Musulmi

IMG 20240310 WA0184(1)

Gwamna Ahmad Aliyu Sakkwato ya sanya hannu ga gyaran dokar rage ikon Majalisar Sarkin Musulmi wadda Majalisar dokoki ta jaha ta amince da ita.

Ahmad Aliyu ya saka hannu ga dokar ne da wasu dokoki 7 yau Alhamis a fadar gwamnati dake Sokoto.

Dokokin sun hada da ta Hukumar Zakka da Waqafi, Hukumar Ilimin Larabci da Addini Musulunci, Hukumar kula da gidajen haya, Hukumar samarda Titunan karkara, Hukumar kula da Asusun Tallafin Tituna da kuma Hukumar kula da masu lalura ta musamman.

Mataimakin Shugaban Majalisar dokoki Hon. Kabiru Ibrahim ne ya jagoranci ‘yan Majalisar dokokin inda suka gabatarwa gwamnan da dokokin da suka amince da su.

Related posts

Leave a Comment