Rahotanni daga Jihar Gombe na bayyana cewar wasu daliban jami’ar Tarayya ta Kashere dake jihar sun bukaci kungiyoyin dalibai na jami’o’i da cewa su rinka samar da shirye-shirye-masu kyau domin jindadin mambobin su.
Daliban sun fadi hakane yayin zantawa dasu a lokacin makon Marhaba na farko da kungiyar dalibai musulmai reshen jami’ar Tarayya ta Kashere ta shirya domin marabtan sabbin dalibai musulmai a jami’ar.
Suna masu cewa samar da shirye-shirye-masu kyau ga dalibai mambobin kungiyoyi a jami’o’i nada matukar muhimmanci wurin karfafa musu gwiwar.
Sun kara da cewar makon Marhaban nada muhimmanci a garesu domin a cewar su sun karu sosai musammam a kasidu daban-daban da aka gabatar a wajen taron.
Da suke karin haske akan makon shugaba da sakataren kungiyar dalibai musulmai reshen jami’ar Tarayya ta Kashere Hamza Muhammad da Abubakar Adam Musa sunce manufar makon itace ilimantar da sabbin dalibai musulmai kan rayuwa a makarantar da kuma bukatar dake akwai ga daliban suyi abunda ya dace domin suyi zarra a fafutukar su ta Neman ilimi.
Dr Umar Muhammad darektan tsare-tsaren karatu na jami’ar Tarayya ta Kashere ya gabatar da kasida mai taken koyon sana’a ita ce ingantacciyar hanya tilo ga dalibai musulmai marasa abunyi.
Wakilin muryar yanchi na Gombe Muhammad Ibrahim Pantami ya ruwaito cewa jami’ar Tarayya ta Kashere dake jihar Gombe na daya daga cikin jami’o’i da gwamnatin tsohon shugaban kasar Nigeria Dr. Good luck Jonathan ya kafa.
