Gawurtaccen Dan Luwadi Zai Zama Alkali A Indiya

Rahotanni daga birnin New Delhi na kasar Indiya na bayyana cewar wani babban kwamitin Kotun ?oli a kasar ya bayar da shawarar na?a wanda ya fito ya bayyana cewa shi ?an luwa?i ne a matsayin al?ali, a wani abin da aka bayyana a matsayin “ci gaba” ga ?ancin masu neman jinsi ?aya, kamar yadda ?ar jarida mai bayar da rahoto kan harakokin shari’a Suchitra Mohanty ta ruwaito.

Kwamitin da babban mai shari’a na ?asar ke jagoranta ya bayar da sunan Saurabh Kirpal domin zama al?alin Babbar Kotun Delhi.

Shawarar babban kwamitin shari’a na daga cikin matakan na?a Al?ali a India kafin daga baya matakin ya samu amincewar gwamnati.

An yi imanin cewa gwamnatin Firaminista Narendra Modi za ta amince da na?in Mista Kirpal a makwanni masu zuwa.

A 2018, Kotun ?olin ?asar ta ?age haramcin luwa?i da Ma?igo a wani hukuncin da aka bayyana babbar nasara ga masu neman jinsi ?aya. Kuma Mista Kirpal shi ne lauyan da ya kare shari’ar da aka shigar.

Related posts

Leave a Comment