Najeriya ta doke Masar da ci 1-0 a rukunin D na gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta 2021.
Dan wasan Najeriya wanda ke buga wasa a Leicester City Kelechi Iheanacho ne ya zura kwallon a minti 30 da soma wasa.
Wasan shi ne mafi zafi kawo yanzu saboda girman ?asashen a tarihin gasar cin kofin Afirka
An yi fafatawar ne a birnin Garoua na Kamaru da misalin ?arfe hu?u na yamma agogon Najeriya da Kamaru.
