Fitina Wadda Ta Zarce Matsalar Tsaro Na Fuskantar Najeriya – Ministan Tsaro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya bayyana cewa ?aruwar matsalar tsaro a Najeriya yana haifar da ?arancin abinci, kuma hakan sabuwar barazana ce dake tunkarar kasar.

Ministan ya fa?i haka ne ranar Litinin a wurin bude wani taro da hukumar tsaro ta fasaha (DIA) ta shirya a Abuja. Ministan yace hare-haren ?ungiyar Boko Haram da ISWAP, da kuma ?alubalen yan bindiga a Arewa ya zama wata babbar barazana ga tsaron Najeriya.

Hakanan Magashi yace satar ?anyen mai a kudu maso kudu da kuma masu fafutukar ?allewa a kudu maso gabas, da fitinar ‘yan awaren Yarbawa masu hankoron kafa yankin Oduduwa suma wata barazana ce ga Najeriya.

“Abin takaicin shine wannan barazana da ake fama da ita na cigaba da zama ?alubale ba wai ga tsaron ?asa da tattalin arziki ba ka?ai, sabuwar barzanar ?arancin abinci ce” “Matsalar abinci shine ya jawo tashin gwauron zabi na farashin kayan abinci a fa?in kasa wanda hakan ya zama wata sabuwar barazana.” “Wannan yasa ya zama wajibi hukumomin tsaro su ha?a kai wajen dakile matsalolin kuma su nemo sabbin hanyoyin gane wasu kalubale da ka iya tasowa a gaba.”

Magashi ya ?ara da cewa nasarorin da jami’an tsaro suka samu kwanan nan yasa yan tada ?ayar baya sama da 14,000 ne suka mi?a wuya tare da aje makamansu.

Related posts

Leave a Comment