Fina-Finai: Jarumi Ahmad S. Nuhu Ya Cika Shekaru 16 Da Rasuwa

A ranar 1 ga watan 1 na shekarar 2023, fitaccen jarumin masana’antar Kannywood Marigayi Ahmad S. Nuhu ya cika shekaru 16 da rasuwa.

Ya rasu a ranar 1 ga watan 1 na shekarar 2007 a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar sa ta zuwa Maiduguri tare da wasu abokan sa su 3, wato Abubakar Didos, Hamza da kuma Ahmad Singa Boy. Wadda kuma Singa Boy din ne kawai ya rage a raye, amma su ragowar Ukun duka sun rasu.

Ya rasu ya bar matar sa, Hafsat Shehu wadda su ka yi aure babu da?ewa.

Masana’antar Kannywood na cigaba da nuna alhini da juyayin wannan babban rashi da ta yi.

Da fatan Allah Ya ji?an shi da rahamarSa. Ya sa aljanna makoma. Amin.

Related posts

Leave a Comment