Farouk Lawan Zai Lashe Shekaru Bakwai A Gidan Yari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya ta zartar da hukuncin ?aurin shekaru bakwai kan Farouk Lawan tsohon ?an Majalisar wakilai daga Jihar Kano kuma tsohon shugaban kwamitin tallafin mai a majalisar wakilai.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta same shi da laifin zargin da ake yi masa na karbar cin hancin a wurin Mista Femi Odetola domin wanke kamfaninsa daga bada?alar tallafin mai

An zargi Lawan ne da karbar dala dubu 620 daga hannun shahararren dan kasuwar, a lokacin da shi Farouk Lawan din yake shugabantar kwamitin binciken badakalar kudaden tallafin mai a shekarar 2012.

Sannan kotun ta bu?aci ya dawo da dala 500,000 ga asusun gwamnatin Tarayyya

Related posts

Leave a Comment