?an-gwagwarmaya, Segun ‘Sega’ Awosanya jagoran Matasa masu Zanga-Zangar SARS, ya sanar da janye hannunsa daga zanga-zangar kawo ?arshen sashe na musamman na ya?i da fashi da makami(#EndSARS) cikin gaggawa.
?an gwagwarmaya ?anchi, wanda ya jagoranci yaki da tozarci da muguntar ?ansanda a shekarar 2017 wanda kuma ya kasance jagaba a zangar-zangar kwanan nan, ya ce zanga-zangar ta sauya akala inda yace ma su wasu manufofi daban-daban sun ?wace ragamar zanga-zangar.
A cikin wata hira da aka yi da shi, ya ?ara da cewa; “duba ga yadda ake kai hari ga manyan mutane da kuma amfani da wannan dama don samar da ku?i ta hanyar ?ungiya mai zaman kanta wadda bata da sahalewar hukuma.
“Hakan gaskiya ya zama barazana ga tsaron ?asarmu da kuma yunkurin mayar da matasanmu ?an tawaye da sunan zanga-zangar kawo ?arshen sashe na musamman mai ya?i da fashi da makami (#EndSARS).
Shin wannan ba rashin hankali bane?” Sakamakon kai hare hare ga jami’an ‘yan sanda da fararen hula gwamnati ta kakaba dokar ta baci ta awanni 24 a jihar Legas.
