EFCC Ta Yi Nasarar Kwato Biliyan 30 A Badakalar Betta Da Halima

images (8)

Hukumar EFCC ta kwato Naira Biliyan 30 Kuma a halin yanzu tana binciken wasu asusun ajiyar banki 50 a wani ?angare na binciken da take yi kan tsohuwar ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu da tsohuwar Shugabar Hukumar NSIPA, Halima Shehu.

Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa ana samun ci gaba a binciken. Ya jaddada muhimmancin lamarin, ya kuma Bu?aci ‘yan Najeriya da su yi hakuri.

“Muna da dokoki da ka’idoji da za su jagoranci binciken mu, su ma ‘yan Nijeriya su fahimci cewa an riga an dakatar da su bisa binciken da muka Gudanar, Kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna aniyarsa ta yaki da cin hanci da rashawa.

“Bugu da ?ari, Dangane da wannan lamari, mun gano sama da Naira biliyan 30, wa?anda aka saka a asusun Gwamnatin tarayya, bincike ya dauki lokaci kafin a kammala shi, mun ?ullo da wannan lamarin kasa da makonni shida da suka wuce, wasu lokuta ana daukar shekaru ana bincike saboda su. Kamata ya yi mu yi nazari a kan bangarori daban-daban da muka bankado, ya kamata ‘yan Nijeriya su ba mu lokaci don gudanar da wannan al’amari yadda ya kamata;

“A halin yanzu muna binciken sama da asusun banki 50 inda muka gano kudade, wannan ba karamin abu bane, yana da matukar muhimmanci, idan aka yi la’akari da karfin ma’aikatanmu da kuma sauran dubban shari’o’in da muke gudanarwa a lokaci daya, ya nuna girman. aikin mu.

“Muna bin diddigin bincike da dama daga bincikenmu. Idan mutane suna sa ran ganin mutane a gidan yari, dole ne su fahimci cewa dole ne a bi tsarin da ya dace. Ya kamata ‘yan Najeriya su yi hakuri da kuma aminta da tsarinmu,” in ji shi.

Related posts

Leave a Comment