Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jihar Ebonyi, daya daga cikin jihohin yankin kabilar Igbo na cikin jihohin da aka fi aurar da kananan yara mata a Najeriya.
Gwamnati ta yi kira ga gwamnan jihar, David Umahi, ya dakile wannan lamari saboda shugaba Muhammadu Buhari ya damu matuka sosai a kai.
Ministar harkokin mata, Mrs Pauline Tallen, ta bayyana hakan ne yayinda ta kai ziyara jihar Ebonyi ranar Juma’a.
Ta ziyarci jihar ne domin kaddamar da shirin rabawa mata rishon girki mai amfani da iskar gas 13,000 ga matan karkara.
An gudanar da shirin ne a Onueke, karamar hukumar Ezza ta kudu a jihar. Tace, “diya mace na kan gaba wajen tsare-tsaren shugaban kasa kuma ina kira gare ku ku bamu hadin kai.” “Ilmantar da diya mace shine abu mafi muhimmanci da gwamnati da iyali zasu iya kuma hakan ya sa gwamnatin tarayya ke kashe kudade da yawa wajen ilmantar da diya mace.”
“Hakazalika, maganar aurar da yara mata ya zama ruwan dare a kasar, kuma jihar Ebonyi har yanzu na daya daga cikin jihohi na gaba.” “Saboda haka ina rokon cewa a magance wannan lamari kuma hanyar yin haka shine tabbatar da cewa yara na zuwa makarantun firamare da jami’a,”.
