Dubban Malamai Sun Yi Addu’ar Samun Shugabancin Kasa Ga Yahaya Bello

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kogi na bayyana cewar fiye da malamai 1,000 na addinin musulunci da kirista sun taru a Abuja ranar Juma’a inda suka nuna goyon bayan su ga gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello Ba anan suka tsaya ba, sun yi masa addu’o’i tare da fatan shi ne zai maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

A cewar su, ya yi aiki tukuru a Jihar Kogi don haka sun yarda cewa zai iya tabbatar da adalci ga kowa idan ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.

Malaman sun ce Bello ne ya dace da ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023 sakamakon ayyukan da suka gani ya yi a Jihar Kogi.

A cewar su, Bello tsayayyen mutum ne wanda zai iya tabbatar da adalci ga ‘yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa. A cewarsu zaman Bello a matsayin magajin shugaba Buhari zai sa ‘yan Najeriya su kasance cikin kwanciyar hankali da hadin kai ba tare da bambancin addini ko yare ba.

Yayin jawabi kamar yadda The Nation ta ruwaito, Bishop Praise Moses ya ce Bello mutum ne mai son zaman lafiya wanda zai bunkasa kasar nan. Moses ya ce Bello yana da ikon yaki da ta’addanci, batagarin ‘yan siyasa, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun jama’a.

A cewar sa, sun yi taron ne don neman yardar Ubangiji akan zabar wa Najeriya shugaba na kwarai. Bishop Moses ya ce: “Ana yakinin da yardar Ubangiji, ta hanyar addu’o’i.

Yayin jawabin Sheikh Abubakar ya ce Gwamnan Bello mutum ne mai gaskiya kuma jajirtacce wanda ake sa ran zai tallafa wa kasar nan idan Buhari ya sauka. A cewar Abubakar, Bello zai samar da tsaro, zaman lafiya da kuma kaunar juna ga ‘yan Najeriya ba tare da bambancin addinai ko kabilu ba.

Don haka yace ya zama wajibi jama’a su zage wurin yin addu’o’i da azumi don gwamnan ya samu nasara inda yace gwamnan yana da duk wasu halaye da musulunci ya ke bukata a wurin shugaban na kwarai.

Related posts

Leave a Comment