Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bu?aci Majalisun Dokokin ?asar su goge sashen da ya hana masu mu?aman siyasa neman takara a cikin sabuwar dokar za?en da ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake sanya wa dokar hannu a fadarsa da ke Abuja.
Sashe na 84 (12) na Dokar Za?e ta 2022 ya bu?aci duk wani mai mu?amin siyasa ya ajiye mu?aminsa kafin ya tsaya wata takara a babban za?e.
Hakan na nufin za a tilasta wa wasu manyan ?usoshin gwamnatin ta Buhari su sauka daga mu?amansu kafin babban za?e na 2023.
Buhari ya ce wasu daga cikin tanadin dokar za su ha?aka harkokin za?e “kamar 3, 9(2), 34, 41, 47, 84(9), (10), (11) da sauransu”.
“Sai dai abin ba haka yake ba… a sashe na 84 (12) wanda ya shatale masu ri?e da mu?aman siyasa game da za?ensu da kuma jefa musu ?uri’a a manyan tarukan jam’iyyu idan ba a gudanar da za?en ba cikin kwana 30 kafin za?e,” in ji shugaban.
