Masana dimokradiyya sun tabbatar da cewa, an samar da ita ne don ta samarwa mutane farin ciki da ‘yanci daga hannayen shugabanni irin na gargajiya wadanda suke da qarfin iko akan komai. Ita kanta kalmar ‘democracy’, da yaren girka tana nufin “Gwamnatin mutane.”
A Najeriya, tun bayan dawowa mulkin dimokradiyya karo na 4, mutane sun sa ran samun sabuwar Najeriya, duba da yadda Allah ya tsareta ba tare da soja ya kuma tankwa6eta ba kamar yadda aka saba gani a baya. Yau a qalla shekara 21 ana yin tsarin a kasar Najeriya. Saidai shekarun basu amfana komai ba, idan aka duba irin damar da aka samu. Da kuma halin da ‘yan kasar suke ciki.
Tunda aka fara dimokradiyya a Najeriya, ake yin kamfen da wuta, ruwa, aikin yi, tsaro, titi, lafiya, ilimi da sauransu. Wadannan abubuwan sune manyan matsalolin ‘yan kasar a yanzu. Abun tambaya a nan shine, mu ba zamu ta6a fita daga cikin rashinsu ba? Shin ina jam’iyar mutane? Ina jam’iyar chanji? Ina bashin da muke kar6owa daga waje tun 1999?
Gaskiya dimokradiyya tayi abun kunya a Najeriya. ‘Ya’yanta na kasar sun kunyatata. Taji jiki kuma ta fad’i ba nauyi. Talaka ya kasa samun farin ciki, bayan ance ita gwamnatin mutane ce, daga mutane, kuma don mutane take rayuwa. Tirrr! Ana 6ata mata suna a Najeriya don an kasa sarrafata wajen samar da cigaba. Abun kunya ne ace, ana yin dimokradiyya amma kuma abubuwa suna qara lalacewa.
Allah ya shiryar damu.
