Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu gungun dattawan Jihar sun yi kururuwar nuna damuwar su a kan sakin gaggan ‘yan bindiga da masu ha?in baki da su, wa?anda su ka zargi jami’an tsaro ke saki a jihar.
Dattawan sun yi kira ga jami’an tsaro su daina sakin ‘yan bindigar da ‘yan-koren su, kuma su ka ?ara da cewa sakin su da ake yi ?in ne ke ?ara munin matsalar tsaron da Zamfara ke fama da ita.
A taron da dattawan su ka yi a Gusau babban birnin jihar ne su ka bayyana wannan damuwa. Sannan kuma sun nuna takaicin su dangane da halin ?uncin da marayun da aka kashe wa iyaye ke ciki, wa?anda yawancin su duk yara ne ?anana ?warai.
Tsohon Sanata, Sa’idu ?ansadau ne ya yi wa manema labarai ta?aitaccen bayani bayan sun kammala taron.
“Wannan kwamiti na dattawan Zamfara ya na mai nuna matu?ar ?acin rai ganin yadda jami’an tsaro ke sakin ‘yan bindigar da aka kama. Ya ce jami’an da ke sakin ‘yan bindigar ko dai wa?anda suka kamo su ke saki, ko kuma wa?anda sojoji su ka kamo su ka dam?a masu. Ko kuma wa?anda ‘yan bijilante su ka kamo su ka dam?a masu.” Inji ?ansadau.
“Muna kira ga jami’an tsaro na cikin jihar nan, don Allah, ku daina sakin ‘yan bindigar da ake kamowa. Ku ri?a gurfanar da su a kotu. Saboda sakin maharan nan bagatatan da ake ta yi, shi ne ya ?ara rura wutar kashe-kashe baya-bayan nan a Zamfara.”
?ansadau ya nemi sake farfa?o da ?ungiyoyin kishin al’umma na cikin jama’a, domin su nemi gudummawar gina makarantun firamare da na sakandare ga ?ananan yaran da ‘yan bindiga su ka kashe wa iyaye, su ka maida su marayu.
?ansadau ya ce an samu ?arin tsaro a Zamfara, lokacin da aka kulle wayoyin sadarwa a jihar Zamfara.
Sai dai kuma ya ce wurare irin su Birnin Magaji, Shinkafi da ?aramar Hukumar Zurmi har yanzu ‘yan bindiga na shigar su kai-tsaye.
Mambobin wannan kwamiti sun ?unshi sarakunan gargajiya, manyan mutanen cikin jihar, malaman addinin musulunci da wasu masu ruwa da tsaki a siyasar jihar Kaduna, su ne su ka ha?a taron musulmai da kiristoci domin a yi addu’ar samun zaman lumana a fa?in jihar.
Sai dai kuma Kwamishinan Harkokin Tsaro Mamman Tsafe, ya ce zargin da dattawan suka yi abu ne mai iya kashe guyawun jami’an tsaron.
