Dalilina Na Daina Rubuta Shirin Fim Din Labarina – Birniwa


S?hahararren marubucin fina-finan Kannywood Ibrahim Birniwa ya ce ya daina rubuta fitaccen fim ?in Labarina mai dogon zango saboda rashin jituwa tsakaninsa da masu shirya shi da kuma aiki kan nasa fim ?in.

D?uk da cewa rashin jituwa ce ta sa marubucin ya fita daga fim ?in, sai dai ya ?i fa?a wa BBC Hausa ainahin abin da ya faru, yana mai cewa “da ni nake rubuta fim ?in da zuwa yanzu ya zo ?arshe”.

D?a yake magana ta cikin shirin Amsoshin Takardunku na Sashen Hausa na BBC a ?arshen mako, Birniwa ya ce ba zai yiwu ya koma rubuta labarin fim ?in ba a nan gaba saboda wasu dalilai.

G?a masu bibiyar fim ?in na Labarina, za su lura da daina ganin sunan Ibrahim Birniwa a cikin marubutansa, inda Nasiru Gwangwazo da Yakubu M. Kumo da Saddika Yahaya da Maimuna Beli suka maye gurbin sa.

B?irniwa ya ce duk da ba salin-alin suka rabu da mashiryan Labarina ba, wanda Aminu Saira ke ba da umarni, amma dai ba baram-baram suka rabu ba kamar taurarin fim ?in Nafisa Abdullahi (Sumayya) da Nuhu Abdullahi (Mahmud).

“?Kafin fim ?in Labarina, mun yi ayyuka da dama da Aminu Saira, wasu manyan fina-finai da ya ba da umarninsu, ni ne na rubuta su, saboda haka muna da ala?ar da ba za a yi baram-baram ba,” in ji shi.

“?Abin da ya faru bai kai a kira shi baram-baram ba duk da cewa ba haka aka so ba. Kamar yadda na fa?a, akwai ayyukana da na saka a gaba.”

Yanzu haka fim ?in Labarina da ake haskawa a tashar Saira Movies ta dandalin YouTube da kuma tashar talabijin ta Arewa 24 na zango na biyar bayan fara haska shi a watan Yulin 2020.

I?brahim Birniwa ne marubucin fim ?in har zuwa tsakiyar zango na uku, kamar yadda ya fa?a wa BBC.

Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar ya ci gaba da rubuta fim ?in, ya amsa da cewa: “Ko da akwai yiwuwar dawowar ma zan ce maka a’a, saboda da ni nake rubuta labarin da na kai shi wajen da ya kamata a ce ya ?are.

“?Sannan ko su da suke rubutawa ma ina tsammanin sun zo ?arshe. Wata?ila sun gama rubuta labarin daga nan har zuwa ?arshe.”

B?BC ta tuntu?i Aminu Saira game da zargin amma ya ce “ba na son saka baki a irin wa?annan maganganun, ba zan ce komai ba”.

B?irniwa ya ce aikin da ya sa a gaba shi ne na ‘Matasa Games’ da ake haskawa a gidan talabijin na Arewa 24, wanda ya ce “yanzu ma aka fara haska shi”.

Related posts

Leave a Comment