Dalilin Da Ya Sa Na Kauracewa Taron PDP – Jonathan

Rahotanni sun tabbatar da Tsohon shugaban ?asa, Goodluck Jonathan, babban jigo a jam’iyyar PDP, bai sami halartar babban gangamin taron PDP na ?asa ba wanda ya gudana ranar Asabar.

An ruwaito cewa Jonathan ya bar Najeriya ranar Asabar domin halartar taron ?ungiyar Nahiyar Africa a Nairobi, Kenya, wanda za’a tattauna kan zaman lafiya a Africa. Amma wasu ?usoshin PDP na ganin tsohon shugaban ya yi amfani da wannan uzurin ne domin tsallake babban gangamin taron PDP.

Wani ?usa a jam’iyyar PDP yace: “Idan har hankalinsa nakan taron, da kuma harkokin jam’iyya da ya halarci wurin na ?an lokaci ya yi jawabi kafin ya tafi ranar Asabar. “Hakanan kuma zai iya turo tsohon mataimakinsa, Namadi Sambo, ko wani na kusa da shi, domin ya yi fatan alkairi a taron a madadinsa.”

Wata majiya daga cikin PDP, ta bayyana cewa gwamnan Bayelsa, Douye Diri, da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, sun gana da Jonathan ranar Jumu’a. Majiyar ta ?ara da cewa lokacin da Jonathan ya fa?a musu zai tafi Nairobi, gwamnonin biyu sun bukaci ya halarci wurin taron na ?an?anin lokaci ya yi jawabi kafin ya tafi.

Hakanan gwamnonin sun masa tayin cewa zasu shirya masa tafiyar da zai yi bayan an kammala taron, amma tsohon shugaban ya ?i amincewa.

Related posts

Leave a Comment