Cikin wata tattaunawa da BBC Hausa tayi da Daraktan shirin fim ?in Kwana Casa’in Salisu T. Balarabe, ya bayyana dalilinsu na sauya tauraruwar shirin Maryuda Yusuf wacce aka fi sani da Salma.
“Lokacin da muka shirya zamu fara ?aukar shirin Kwana Casa’in Zango na shida mun tuntu?i Salma, sai ta fa?a mana cewa gaskiya ba za ta samu dama ba.”
“Mun so mu san dalili sai ta fa?a mana cewa yana da nasaba da iyayenta wanda ba lallai ne ta iya bayyanawa ba.” Inji Darakta T. Balarabe
