Babban lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami SAN ya kare matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na kin bayyana masu daukar nauyin Boko Haram
Yace daukar matakin ya zama dole dan kada a kawowa binciken da ake yi cikas.
Kakakin Malami, Umar Gwandu ne ya bayyana haka inda yace malamin ya fadi hakane a birnin New York.
An caccaki gwamnatin tarayya saboda kin bayyana sunayen wadanda ke daukar nauyin Boko Haram din.
