Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya yi bayani a kan dalilin da yasa ya raba jiha da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC mai mulki.
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, a yayin wata tattaunawa ta Twitter wanda daya daga cikin jagororin zanga-zangat #EndSARS, Rinu Oduala ya shirya.
Saraki, shugaban majalisar dattawa a majalisa ta takwas daga 2015 zuwa 2019 ya amsa tambayoyi daga mutane kan zaben 2023 da kuma harkokin siyasa na baya.
A cewarsa, ya goyi bayan takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 saboda yana burin ganin chanji a kasar amma abin takaici sai ya gamu da akasi.
Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ambaci abubuwan kamar haka:
1. Tsangwama Saraki ya yi ikirarin cewa ya sha tsangwama a lokacin da yake matsayin shugaban majalisar dattawa saboda ya tsaya tsayin daka don ganin yancin majalisar dokokin tarayyar.
?an takarar shugabancin kasar ya bayyana cewa dukkanin wahalar da ya sha ya kasance saboda majalisar dokokin tarayya a karkashin jagorancinsa bata yarda da yiwa bangaren zartarwa alfarma ba.
2. Saraki ya bayyana cewa gazawar gwamnatin Buhari karkashin APC wajen kawo chanjin da ake bukata ne ya sa shi barin jam’iyyar.
3. Alkawarin chanji A cewarsa, ya zata ajandar chanji na jam’iyyar za ta taimake shi wajen cimma manufofinsa don amfanin yan Najeriya gaba daya.
4. Ba a cimma manufar chanji ba Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce ya bar tafiyan ne a lokacin da ya lura cewa manufar chanji da jam’iyyar ta yiwa yan Najeriya alkawari ba a gani a kasa ba.
