Dakatar Da Kyari: ‘Yan Najeriya Na Cigaba Da Bayyana Ra’ayoyin Su

Tun bayan sanarwar da hukumar ‘yan sandan Najeriya ta bayar na dakatar da jami’in ‘yan sanda Abba Kyari, jama’a ke cigaba da bayyana ra’ayoyin su dangane da yadda suke kallon lamarin.

Abdullahi Muhammad Sani wani mai sharhi ne a Najeriya ga abin da ya rubuta dangane da yadda yake kallon al’amarin.

“A ce duk lokacin da mutum zai bada rayuwar shi domin Nijeriya ta ci gaba sai ya samu kalubale daga makiya zaman lafiya?”

“Kowa ya san irin kokarin da Abba Kyari yake yi domin zaman lafiyar kasar nan, amma duk da haka sai da aka bari suka cimma burinsu akanshi”.

Allah sarki Arewa! Muna cikin yanayi na rashin tabbas domin na lura duk wani dan Arewa da ‘yan kudu suka sako shi gaba sai an ba su kofa sun ga bayan shi. Yau inda a ce Abba Kyari dan kudu ne wallahi da ba za a dakatar da shi da garaje ba, amma saboda mu ‘yan Arewa ba su da kishi gashi nan sun bari an dakatar da shi’

Shima anashi ?angaren tsohon ?an Majalisar Dattawa mai wakiltar maza?ar Kaduna ta tsakiya Shehu ya yi tsokaci ne akan al’amarin kamar haka.

“?AN AREWA MUNAFUKKAI NE: Kun ji dadi an kama Nnamdi Kanu da Sunday Igboho amman kuma baku ji dadin kama Abba Kyari ba”

Sanatan ya ce akwai munafurci a cikin zukatan ‘yan Arewa, domin an kama Sunday Igboho da Nnamdi Kanu sun ji dadi amman saboda munafurci ana tuhummar Abba Kyari sun ji haushi sun dami mutane da surutu.

Related posts

Leave a Comment